Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bayyana cewa ta cafke mutum 107 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban cikin watan da ya gabata.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ibrahim Bakori, ne ya sanar da hakan a hedikwatar rundunar da ke Bompai a ranar Litinin, ga manema labarai.
Ya ce daga cikin waɗanda aka kama akwai masu fashi da makami 8, masu garkuwa da mutane 8, masu safarar mutane 3 da kuma masu safarar miyagun ƙwayoyi 14. Haka kuma an kama masu satar motoci 2, masu satar babura 6, barayi 5 da kuma matasa 61 da ake zargi da tada rikici “Yan Daba”. An kuma ceto mutum ɗaya da aka yi garkuwa da shi.
Rundunar ta kuma gano bindiga AK-47 guda ɗaya, bindigogi kirar gida 7 motoci 7, babura 8 da shanu 7.
Kwamishinan ya ce tun bayan kaddamar da Operation Kukan Kura daga 1 ga Yuli, 2025 zuwa yanzu, an kwato makamai 473 da kuma miyagun ƙwayoyi masu tarin yawa.



