DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Jami’ar UDUS za ta karrama Sheikh Daurawa da digirin girmamawa

-

Jami’ar Usmanu Danfodiyo Sokoto (UDUS) ta sanar da cewa za ta karrama fitaccen malamin addinin Musulunci Sheikh Muhammad Aminu Ibrahim Daurawa, wanda za a ba shi digirin girmamawa na Doctor of Letters (D.Litt), Honoris Causa.

Wannan karramawa na zuwa ne bisa jajircewarsa wajen ilimi, gyaran zamantakewa, da kuma kokarinsa na yada zaman lafiya a Najeriya da ma kasashen waje.

Shugaban Jami’ar Farfesa Bashir Garba ne ya bayyana hakan, a yayin taron manema labarai gabanin bikin cikar jami’ar shekaru 50 da kuma yaye daliban da suka kammala karatu karo na 42.

Haka kuma, tsohon Shugaban Sojojin Najeriya, Laftanar Janar Faruku Yahaya (Rtd.), zai samu lambar girmamawa ta Doctor of Science (D.Sc.), Honoris Causa, bisa gudummawarsa ga harkokin tsaro da kare martabar kasa.

Jami’ar ta bayyana cewa wannan karramawa wani yunkuri ne na girmama mutanen da suka sadaukar da rayuwarsu wajen raya kasa, ilimi da zaman lafiya.

Bikin zai kasance babban abin tarihi yayin da dubban dalibai za su karɓi takardunsu, tare da nuna irin gudummawar UDUS ga ci gaban ilimi da zaman lafiya a Najeriya tun daga 1975 zuwa yau.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttp://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Babban Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.

1 COMMENT

  1. Wannan karramawa da Jami’ar UDUS za tayi wa Sheikh Daurawa gaskiya abin a yaba ne duma da irin Gudunmawar da yake bayarwa ta ko wane Bangare. Ubangiji Allah ya qaro mana Ilimi mai amfani

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Obasanjo ya nuna jarumtaka da sadaukarwa wajen yi wa Nijeriya hidima – Shugaba Tinubu

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, ya taya tsohon shugaban ƙasar Olusegun Obasanjo murnar cika shekaru 89 da haihuwa. A cikin wata sanarwa da mai magana da...

China ta umurci matatun man fetur din ta su dakatar da jigilar sa saboda rikicin Gabas ta tsakiya

Gwamnatin China ta umurci manyan matatun man fetur na ƙasar da su dakatar da fitar da dizal da fetur zuwa ƙasashen waje na ɗan lokaci,...

Mafi Shahara