Sanata Kabiru Marafa ya zargi shugaban Nijeriya Bola Tinubu da yin siyasar amfani da mutane tare da watsar da su, yana mai cewa hakan ya bayyana a yadda aka yi wa tsofaffin gwamnonin Nasir El-Rufai, Abdullahi Ganduje da kuma shi kansa.
Marafa ya bayyana hakanne a gidan talabijin na Channels, ya ce siyasa ba bauta ba ce, illa dama ta yi wa al’umma hidima.
Ya jaddada cewa zai ci gaba da zama ne kawai idan an ba shi damar kawo ayyukan alheri ga mutanen mazabarsa.



