Matar da ke aikin shara da goge-goge a asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri Faiza Abdulkadir, wadda ta mayar da naira miliyan 4.8 da aka tura mata a asusun bankinta bisa kuskure, ta samu kyautar naira miliyan 2.5 daga wani mutum da ba a bayyana sunansa ba.
An mika mata wannan tallafi ne a ranar Litinin a Maiduguri ta hannun shugabar ƙungiyar Da’awah Wal Irshaad Women Organisation ta jihar Borno, Hajiya Aisha Muhammad Aisami, wadda ta ce mutumin ya karanta labarin matar ne a jaridar Daily Trust sannan ya bukaci a nemo ta domin a karfafa mata gwiwa.
A matsayin ta na ma’aikaciyar asibitin, Fa’iza na samun albashin N30,000 kacal a kowane wata, tana kuma daukar nauyin mahaifiyarta da kuma ‘ya’yanta guda biyar.
Tun da fari matar gwamnan jihar Borno, Dr Falmata Babagana Zulum, ta yi mata kyautar Naira miliyan guda tare da kayan abinci da kayan koyon sana’o’in dogaro da kai.



