Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta ayyana ranar Juma’a, 5 ga Satumban 2025 a matsayin ranar hutu domin bikin Maulidi, wato ranar tunawa da haihuwar Manzon Allah, Annabi Muhammad (SAW).
Ministan harkokin cikin gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo ne ya sanar da hakan a madadin gwamnatin cikin wata sanarwa da sakatariyar ma’aikatar, Dr. Magdalene Ajani ta fitar.
Tunji-Ojo ya taya al’ummar Musulmi a Nijeriya da ma duniya murna, inda ya yi kira da su yi koyi da kyawawan halayen Annabi (SAW) na zaman lafiya, ƙauna, tawali’u, haƙuri da jin ƙai.
Haka kuma, ministan ya bukaci ’yan Nijeriya masu bin addinai daban-daban da su yi amfani da wannan dama wajen roƙon Allah domin samun zaman lafiya, tsaro da kwanciyar hankali, tare da mara wa gwamnati baya wajen tabbatar da haɗin kai da ci gaban kasar baki daya.



