Shugaba Bola Tinubu ya umarci sakataren gwamnatin tarayya da ya fitar da takardar umarni ga dukkan ma’aikatu da hukumomi domin tabbatar da inshorar lafiya bisa tanadin dokar inshorar lafiya ta shekarar 2022.
Sai dai shugaban kasar ya jaddada bukatar ci gaba da tattaunawa da ɓangarori masu zaman kansu domin tabbatar da cewa dokar ba ta kawo tangarda ga kowane bangare ba.
Ya ce dukkanin ma’aikatu da hukumomi za su sanya ma’aikatansu a tsarin, kuma duk wani kamfani ko kungiya da ke son kulla alaka da gwamnati dole sai ya gabatar da takardar shaida da hukumar inshorar lafiya NHIA ta bayar, yana mai cewa idan babu ita gwamnati ba za ta kulla wata yarjejeniya da wani kamfani ko kungiya ba.



