An sake samun faduwar babban layin wutar lantarki “National Grid” na Nijeriya a yau Laraba, lamarin da ya jefa al’umma cikin halin rashin wuta a sassa daban-daban na ƙasar.
Kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja Electricity Distribution Company AEDC ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X da misalin ƙarfe 11:23 na safe.
Sanarwar da kamfanin ya fitar ta ce rashin wutar da ake fama da shi yanzu ya samo asali ne daga faduwar babban layin, kuma ana kokarin shawo kan matsalar.
Jaridar Punch ta rawaito cewa har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a bayyana musabbabin faruwar lamarin ba.



