DCL Hausa Radio
Kaitsaye

ADC ta karyata rahoton kotu kan shugabanninta

-

Jam’iyyar ADC ta bayyana cewa babu wani umarnin kotu da aka bayar a kan sabon shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata David Mark, da sakataren jam’iyyar na kasa, Tsohon Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa magana da yawun jam’iyyar na kasa, Bola Abdullahi, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis, inda ya ce bayan gazawar wasu masu son zuciya wajen hana INEC amincewar da sabon shugabancin jam’iyyar, yanzu sun koma yada labaran karya.

Google search engine

ADC, wacce ke kan gaba cikin jam’iyyun adawa a Najeriya, ta shiga rikicin shugabanci a ‘yan watannin nan, lamarin da ya kara kamari bayan hukumar INEC ta tabbatar da sabon shugabancin jam’iyyar karkashin David Mark a matsayin shugabanta na kasa da kuma Rauf Aregbesola a matsayin Sakataren Kasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Obasanjo ya nuna jarumtaka da sadaukarwa wajen yi wa Nijeriya hidima – Shugaba Tinubu

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, ya taya tsohon shugaban ƙasar Olusegun Obasanjo murnar cika shekaru 89 da haihuwa. A cikin wata sanarwa da mai magana da...

China ta umurci matatun man fetur din ta su dakatar da jigilar sa saboda rikicin Gabas ta tsakiya

Gwamnatin China ta umurci manyan matatun man fetur na ƙasar da su dakatar da fitar da dizal da fetur zuwa ƙasashen waje na ɗan lokaci,...

Mafi Shahara