Tsohon Attorney janar kuma ministan Shari’a na tarayya, Abubakar Malami (SAN, CON), wanda kuma shi ne jagoran jam’iyyar ADC a Jihar Kebbi, ya rubuta ƙorafi ga mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro (NSA), shugabannin DSS, ’Yan Sanda, Hukumar Shige da Fice, da Civil Defence domin nuna bukatar gaggawar da lamarin ke da shi.
A cewar ƙorafin, wanda aka sanya wa kwanan watan ranar 10 ga Satumba, 2025, Malami ya yi zargin cewa wasu ’yan siyasa suna haɗin gwiwa da ’yan banga daga Jamhuriyar Nijar tare da basu makamai ta haramtattun hanyoyi.
Ya bayyana cewa ana ‘yan siyasar na shirin tura batagarin domin kai wa jama’a hari, hana ‘yan adawa sakat, da kuma lalata zaman lafiya a jihar.
Malami ya roƙi NSA da sauran shugabannin tsaro da su ɗauki matakan gaggawa ta hanyar haɗa kai tsakanin hukumomin tsaro, tsare iyakokin ƙauyuka don hana shigar ’yan banga da makamai, tare da kaddamar da bincike na musamman kan zargin haɗin guiwar wasu jami’an gwamnati da ’yan ta’adda.



