Gwamnatin Ogun karkashin jagorancin gwamna Dapo Abiodun ta nada mutane 1200 domin taimaka mata wajen kawo sauyi a jihar.
Cikin wata sanarwa da gwamnan ya fitar ta hannun mataimakinsa Kayode Akinmade, ya ce wannan yunkuri ne na gwamnatinsa wajen ganin ta yi tafiya da kowane dan jihar a tsari irin na dimukuradiyya.
An zabo mataimaka biyar daga kowace mazaba cikin 236 da ake da su a fadin jihar, kamar yadda Channels TV ya wallafa.
Gwamnan ya bukaci mataimakan nasa su kasance masu bayar da kowacce irin gudunmawa wajen ganin an ciyar da jihar ta Ogun gaba.



