Mataimakin direban jirgin kamfanin Air Peace ya yi watsi da binciken da hukumar NSIB ta gudanar kan su, wanda ya nuna cewa suna shan barasa tare da tu’ammali da ƙwayoyi.
Lamarin ya samo asali ne bayan da jirgin na Air Peace mai dauke da fasinjoji 103, ya sauka ba daidai ba a filin sauka da tashin jirage da ke Fatakwal.
Sai dai yayin da ake hira da shi a gidan talabijin na Arise, mataimakin matukin jirgin David Bernard, ya ce hukumar NSIB ta gudanar da binciken ta a cibiyar da ba ta da rajista, da nufin bata sunan kamfanin, kamar yadda jaridar punch ta ruwaito.



