Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta bayyana cewa tana kan hanyar bunkasa shirin ciyar da dalibai a makarantun da ke fadin kasar.
Jagorar shirin Aderemi Adebowale ce ta bayyana haka yayin da take tattaunawa da kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN a Abuja, inda ta ce gwamnati na da burin ciyar da daliban firamare akalla miliyan 50 a makarantu daban daban da ke fadin kasar a shekarar 2026.
A cewar ta, yaran da basa zuwa makaranta ma ba za a bar su a baya ba, domin gwamnatin na shiri a kan su, kamar yadda jaridar punch ta ruwaito.



