Wasu masu kasuwancin fetur a Nijeriya sun yi zargin cewa fataken man fetur na kasashen waje na samun ragin N65 kan kowace lita daga matatar man Dangote kan yadda ake saida wa na cikin kasar.
Yayin tattaunawa da jaridar Punch ne kungiyoyin DAPPMAN da PETROAN suka tabbatar da haka.
A cewar kungiyar DAPPMAN, rage farashin mai da matatar Dangote ta yi ba wani abu bane face yunkurin sa gasa a bangaren na fetur ta kara zama mai matukar wahala.



