Daidai lokacin da wa’adin dokar ta baci ke shirin karewa a Ribas, dattawan jihar sun nuna shakku kan yiwuwar dawowar Siminalayi Fubara cikin karsashi.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa har zuwa wannan lokaci da ya rage ‘yan kwanaki kantoman jihar Ibok-Ete Ekwe Ibas mai ritaya ya yi bankwana da gidan gwamnati, ba a samu wata sanarwa ko tattaunawa daga wajen Fubara ba.
Sai dai wani mataimakinsa wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya bayyana wa jaridar cewa Fubara zai sauka a jihar cikin ranakun karshen mako, domin ci gaba da jagoranci a matsayin gwamna.



