DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Sarki Sanusi ya gargadi gwamnatin tarayya kan yawan ciyo bashi

-

Sarkin Kano na 15, kuma tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya CBN Muhammadu Sanusi II, ya nuna damuwa kan yadda gwamnatin tarayya ke ci gaba da ciyo bashi ba tare da tsari ba.

Sarki Sanus ya yi wannan bayani ne a bikin Kano International Poetry Festival KAPFEST a Kano, inda ya ce bashin da ake bin Nijeriya ya kai Naira tiriliyan 150 a farkon shekarar 2025 zai iya jefa ƙasar cikin mummunar matsalar kuɗi nan da shekaru 20.

Google search engine

Sarki Sanusi ya yi gargadi cewa idan ba a yi amfani da wadannan makudan kudade wajen inganta ilimi da ƙarfafa matasa ba, abin ba zai yi wa kasar kyau ba.

Ya kuma ce maimakon duk waÉ—annan basussukan a yi amfani da su ne wajen koyar da matasa domin su ne za su biya shi, amma abin takaici ana cin bashin ba tare da saka hannun jari ba.

Sai dai ya yaba wa matakin cire tallafin man fetur, yana mai cewa hakan ya ceci ƙasar daga fadawa matsalar tattalin arziki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Obasanjo ya nuna jarumtaka da sadaukarwa wajen yi wa Nijeriya hidima – Shugaba Tinubu

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, ya taya tsohon shugaban ƙasar Olusegun Obasanjo murnar cika shekaru 89 da haihuwa. A cikin wata sanarwa da mai magana da...

China ta umurci matatun man fetur din ta su dakatar da jigilar sa saboda rikicin Gabas ta tsakiya

Gwamnatin China ta umurci manyan matatun man fetur na ƙasar da su dakatar da fitar da dizal da fetur zuwa ƙasashen waje na ɗan lokaci,...

Mafi Shahara