Kamfanin rarraba wutar lantarki na Kano KEDCO ya bukaci Asibitin koyarwa na Aminu Kano AKTH ya biya bashin wutar da ya sha wacce ta kai Naira miliyan 949.88 a watan Augusta, tare da kudin watan nan na Satumba 108.95m cikin kwanaki goma ko a katse musu wuta.
A cewar mai magana da yawun kamfanin, Sani Bala, asibitin ya kasa biyan kudin wutar da ake amfani da ita a gidajen ma’aikata, lamarin da ke shafar ingancin ayyukan KEDCO.
Jaridar Punch ta rawaito cewa KEDCO ya tabbatar da cewa manyan cibiyoyin lafiya a asibitin suna samun wuta daga 33KVA da ke ba da kimanin sa’o’i 22 na wuta a kowace rana.
Sai dai kamfanin na KEDCO ya ce kin amincewar AKTH a raba layukan wutar lantarki ta barngaren asibitin da gidajen ma’aikata ne ya jawo matsalolin katsewar wuta a kwanakin baya.