Akalla mutane 40 ne ake zargin ’yan bindiga sun sace da Asuba a wani masallaci da ke kauyen Gidan Turbe, ƙaramar hukumar Tsafe, jihar Zamfara.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 5:30 na asubar ranar Litinin yayin da suke tsaka da sallah.
Wannan harin ya nuna rushewar yarjejeniyar sulhu da aka kulla a watan da ya gabata tsakanin shugabannin al’umma da wasu daga cikin ’yan bindiga a Katsina da Zamfara.
Yarjejeniyar dai ta yi alƙawarin kawo ƙarshen hare-hare da garkuwa da mutane, tare da ba manoma damar yin noma a gonakinsu cikin kwanciyar hankali.
Sai dai kwatsam, wasu daga cikin ’yan bindigar sun ci gaba da kai hare-hare a jihohin arewa maso yamma.
Daily Trust ta rawaito cewa rahotanni sun tabbatar da dakarun Operation fansar yamma na ci gaba da sintiri da kai samame a yankunan da abin ya shafa.