Jam’iyyar APC a Ribas ta bayyana shirinta na yunkurin janyo dakataccen gwamnan jihar Siminalayi Fubara cikinta, daidai lokacin da yake daf da karbar ragamar ci gaba da gudanar da mulki.
Mai magana da yawun jam’iyyar na jihar Darlington Nwauju ne ya bayyana haka a gidan talabijin na Channels, kamar yadda jaridar punch ta ruwaito.
A cewar sa, muddin Fubara ya koma cikin jam’iyyar ta su, to tabbas zai kasance wanda zai ci gaba da jan ragamar APCn a jihar.
A ranar Alhamis mai zuwa ne ake sa ran cewa Fubara zai koma jihar ta Ribas domin karɓar ragama a matsayin gwamnan jihar.



