Gwamnatin Katsina ta ce an samu raguwar ayyukan ta’addanci da kaso 70 a fadin jihar, biyo bayan daukar muhimman matakai wajen kawo karshen matsalar tsaron da ke addabar sassan ta.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Dr. Nasir Mu’azu ne ya bayyana haka yayin wani muhimmin taron bayar da rahoton halin da ake ciki kan tsaro, wanda gwamna Dikko Umaru Radda ya shirya.
Wata sanarwa da fadar gwamnatin jihar ta fitar, ta bayyana cewa irin matakan da gwamnatin ke dauka ya sanya da yawa daga cikin jagororin ‘yan bindiga ajiye makamansu tare da neman a yi sulhu.
Sanarwar ta kuma ce jagororin al’umma na ci gaba da yunkurin daukar gabaren yin sulhu da’ yan bindiga a wasu karin yankunan jihar.



