Majalisar dokokin Chadi ta amince da kara wa’adin mulkin kasar daga shekaru biyar zuwa bakwai, tare da bayar da damar tsayawa takara babu kayyadewa.
‘Yan majalisar dokokin kasar 171 ne suka amince da yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima, inda sabuwar dokar ta yi tanadin karin wa’adi ga su kansu’ yan majalisar, har ma da kirkirar kujerar mataimakin Firaminista.
A halin yanzu dai za a gabatar da wannan sabuwar doka ga ‘yan majalisar dattawan kasar domin kada kuri’a kafin ta fara aiki nan take.



