DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Yan Arewa na da ‘yancin karawa da Tinubu a takarar shugaban kasa – ACF

-

Kungiyar dattawan Arewa ACF, ta mayar da martani kan kiran da gwamnan jihar Neja, Umaru Bago, ya yi na cewa ’yan siyasar Arewa su bari sai bayan shekara ta 2031 kafin su nemi shugabancin ƙasar.

A cewar Gwamna Bago, ya kamata a bar Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda ya fito daga Kudu, ya kammala wa’adin mulkinsa na shekara takwas kafin wani daga Arewa ya fito takarar shugaban ƙasa.

Google search engine

Sai dai sakataren yaɗa labaran kungiyar na kasa, Tukur Muhammad-Baba, ya bayyana cewa wannan magana ta Bago ba ta da wata madogara a kundin tsarin mulkin Najeriya.

Inda ya ce kundin tsarin mulki ya baiwa kowanne ɗan ƙasa damar tsayawa takara ko a zaɓe shi, babu wani tanadi da ya ce sai a dagawa wani kafa a neman takara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Obasanjo ya nuna jarumtaka da sadaukarwa wajen yi wa Nijeriya hidima – Shugaba Tinubu

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, ya taya tsohon shugaban ƙasar Olusegun Obasanjo murnar cika shekaru 89 da haihuwa. A cikin wata sanarwa da mai magana da...

China ta umurci matatun man fetur din ta su dakatar da jigilar sa saboda rikicin Gabas ta tsakiya

Gwamnatin China ta umurci manyan matatun man fetur na ƙasar da su dakatar da fitar da dizal da fetur zuwa ƙasashen waje na ɗan lokaci,...

Mafi Shahara