DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Kotu a Abuja ta yi watsi da bukatar hana hukumar ICPC bincike a Kano

-

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da ƙarar da wasu jami’an ma’aikatar Ilimi mai zurfi ta jihar Kano suka shigar, inda suka nemi hana Hukumar ICPC bincike kan zargin amfani da kuɗaɗen tallafin karatu ba bisa ka’ida ba.

Mai shari’a J. Obanor ya ce gayyatar da ICPC ta yi na neman takardu ba take hakkin kowa ba, ya kuma tabbatar da ikon hukumar na ci gaba da gudanar da binciken da take gudanarwa a hukumar.

Google search engine

A yayin binciken, ICPC ta gayyaci jami’an Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi ta Kano da Hukumar Tallafin Karatu ta jihar domin gabatar da takardu da kuma yi wa hukumar bayani.

Sai dai maimakon amsa gayyatar, jami’an a karkashin Dr. Hadi Bala, babban sakatare na ma’aikatar, ya jagoranta, suka shigar da ƙara mai lamba CV/2857/2025 kan babban lauyan ƙasa da ICPC, suna ikrarin irin waɗannan gayyatar cewa tauye musu ’yanci ne, lamarin da kotun ta musanta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Obasanjo ya nuna jarumtaka da sadaukarwa wajen yi wa Nijeriya hidima – Shugaba Tinubu

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, ya taya tsohon shugaban ƙasar Olusegun Obasanjo murnar cika shekaru 89 da haihuwa. A cikin wata sanarwa da mai magana da...

China ta umurci matatun man fetur din ta su dakatar da jigilar sa saboda rikicin Gabas ta tsakiya

Gwamnatin China ta umurci manyan matatun man fetur na ƙasar da su dakatar da fitar da dizal da fetur zuwa ƙasashen waje na ɗan lokaci,...

Mafi Shahara