Rahotanni sun bayyana cewa jirgin ruwan, wanda mafi yawancin fasinjojin sa mata ne, ya yi hatsari ne da misalin ƙarfe 7:30 na yamma ranar Alhamis, yayin da suke kokarin tserewa daga harin ‘yan bindiga.
Rahoton jaridar Daily Trust ya ce jirgin ya kife a gefen wata gada kafin daga bisani ya kife.
A halin yanzu, masu aikin ceto na ci gaba da aikin gano wadanda hatsarin ya rutsa da su da kuma tantance adadin mutanen da suka rasu.



