Tun bayan tafiyar Vice Admiral Ibok-Ekwe Ibas mai ritaya, wanda ya yi aiki a matsayin kantoman riko na jihar, an yi ta samun rudani game da dalilin rashin dawowar gwamnan a kan lokaci.
Rahoton jaridar Daily Trust ya ce magoya bayan gwamnan sun taru a gidan gwamnati, da ke birnin Port Harcourt, domin tarbar sa.
Amma daga bisani suka watse bayan jiran sa na sa’o’i masu yawa. Sai dai da safe sun sake komawa filin jirgin sama na Port Harcourt International Airport, Omagwa, inda jirgin da ya ɗauko gwamnan ya sauka da misalin ƙarfe 12 na rana.
Bayan gaisawa da magoya bayansa a sashen manyan baki na filin jirgin, gwamnan ya shiga cikin ayarin motocin sa ya wuce.
Har yanzu ba a tabbatar ko zai zarce kai tsaye zuwa gidan gwamnati domin fara aiki ba.



