Wani jigo a jam’iyyar PDP, Dan Ulasi, ya bayyana cewa zai yi farin ciki idan Peter Obi ya koma jam’iyyar PDP gabanin zaɓen 2027.
Jaridar Punch ta ruwaito shi, yayin da yake zantawa da gidan talabijin na Arise a ranar Juma’a, inda ya ce kwarjini da farin jinin Obi zai ƙarfafa damar PDP ta lashe zaɓen mai zuwa.
Dangane da batun tsarin karba-karba, Ulasi ya yi kira da a yi adalci wajen zaɓar ɗan takarar shugaban ƙasa a 2027, inda ya ce PDP ta riga ta yarda da cewa shugaban ƙasa ya fito daga kudu, kuma ya dace a ƙara takaita shi zuwa kudu maso gabas domin ita ce kadai yankin da bai taba samar da shugaban ƙasa a tarihin Najeriya ba.



