Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa an samu ci gaba a tattaunawarsa da shugaban kasar China Xi Jinping kan batun sayar da manhajar TikTok, tare da sanar da niyyarsa ta kai ziyara kasar nan gaba.
Shugabannin kasashen biyu mafi girma a duniya sun yi waya karo na biyu tun dawowar Trump fadar White-House.
Duk da matsanancin suka da ya sha yi wa kasar Sin a baya, yanzu yana ƙoƙarin rage zafin rikice-rikicen diflomasiyyar da ke tsakani.
Rahoton jaridar Punch ya ce a daya hannun, gwamnatin kasar Sin ta fitar da jawabi mai É—an tsauri, inda ta bayyana matsayinta a fili.



