Gwamnan Ribas Siminalayi Fubara ya bayyana cewa neman zaman lafiya, daidaito da kuma ci-gaba ne ya sanya shi kin kalubalantar dokar ta bacin da shugaba Tinubu ya ayyana a jihar.
Gwamnan ya yi wannan furuci ne a jawabinsa ga ‘yan jihar a ranar Juma’a, biyo bayan karewar wa’adin dokar da shugaban ya ayyana, kamar yadda jaridar punch ta ruwaito.
A cewar Fubara, ya fuskanci matsi daga magoya bayansa domin ya kalubalanci dokar, sai dai ya ki amincewa da hakan.
Kwanaki biyu bayan janye dokar ne gwamnan da mataimakiyarsa tare da shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar ta Ribas suka sauka a filin sauka da tashin jirage na Fatakwal.



