Rahotanni daga cibiyar da ke kula da harkar ƙwayoyi a India, sun tabbatar da cewa ‘yan Najeriya 106 na daga cikin ‘yan kasashen waje 660 da aka kama a shekarar da ta gabata, kan zargin su da safarar miyagun ƙwayoyi a kasar.
Yayin wani taron masu ruwa da tsaki da daga sassa daban daban na kasar, ministan cikin gida na India Amit Shah, ya ce’ yan kasar Nepal 203 aka kama, wadanda suka fi kowa yawa, sai kuma ‘yan Myanmar 25, kamar yadda Channels TV ya wallafa.
Rahoton ya kuma ce akwai ‘yan kasashen Bangladesh 18, Ivory Coast 14, Ghana 13 sai kuma ‘yan Iceland 10 da aka kamar kan zarge-zargen tu’ammali da miyagun ƙwayoyin.



