Mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima ya bar Abuja zuwa birnin New York na Amurka domin jagorantar tawagar kasar zuwa taron majalisar dinkin duniya karo na 80
A cewar mataimaki na musamman ga Kashim Shettima, Stanley Nkwocha, mataimakin shugaban kasar zai wakilci shugaba Tinubu wajen gabatar da jawabin Najeriya a yayin taron.
Za a gudanar da taron ne daga ranar Litinin 22 zuwa Lahadi 28 ga watan Satumban 2025.



