Majalisar Dattawan Nijeriya ta buɗe ofishin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, wanda aka rufe tsawon watanni shida sakamakon dakatar da ita.
Rahotanni sun nuna cewa ofishin nata da ke a ginin majalisar dattawa an buɗe shi ne a ranar Talatar nan.
Wannan na iya zama alamar cewa za ta dawo bakin aiki, yayin da majalisar ke komawa daga hutun da take a ranar 7 ga Oktoba, 2025.
A makon da ya gabata, Sanata Natasha ta rubuta wa shugabancin majalisar dattawa wasiƙa, inda ta sanar da niyyarta ta komawa bakin aiki bayan shafe tsawon watanni shida bisa dakatarwar da aka yi mata.



