Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi alkawarin sanya muradun al’ummar Yarbawa a saman jerin ajandar mulkinsa idan ya lashe zaben shugaban ƙasa na 2027.
Atiku ya musanta maganganun da ake yadawa cewa mulkinsa zai bada fifiko ga Hausa/Fulani a kan Yarbawa ko sauran kabilun Nijeriya.
A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Kola Johnson, ya fitar a Abuja ranar Alhamis, Atiku ya ce yana da zumunci mai karfi da Yarbawa da iyalai da abokan arziki.
Don haka ya kara da cewa, alaƙar aure kadai ta isa ta kawar da duk wani tsoro ko fargaba na cewa mulkinsa zai kawo wariya da ƙabilanci tsakanin kabilun kasar.