Hukumar kula da harkokin man fetur ta Nijeriya (NUPRC) ta bayyana cewa yanzu haka Najeriya na da ƙarfin samar da ganga miliyan 2 na man fetur a kowace rana.
Sai dai hakan ya yi ƙasa da burin gwamnati na fitar da ganga miliyan 2.2 a kowace rana kamar yadda aka tsara a kasafin kudin shekarar 2025.
A wata sanarwa da hukumar ta fitar jiya Laraba, ta ce Najeriya na kan hanyar cika adadin da OPEC ta ware mata, sakamakon wasu matakai da aka ɗauka tare da haɗin gwiwa da masu ruwa da tsaki a masana’antar domin ƙara yawan adadin.



