Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya NLC ta umarci dukkan ƙungiyoyin da ke ƙarƙashinta da su fara wayar da kai da shirye-shiryen shiga yajin aikin ƙasa baki ɗaya kan kamfanin Dangote, tana zarginsa da tauye haƙƙin ma’aikata.
Wannan na zuwa ne bayan yajin aikin da ƙungiyar manyan ma’aikatan man fetur da gas PENGASSAN ta fara a ranar Litinin a kan matatar man Dangote, wanda ya durƙusar da harkokin manyan hukumomin kula da man fetur da gas a ƙasar, ciki har da NNPCL, NUPRC da kuma NMDPRA.
A ranar Litinin ɗin ma, kotun kwadago ta ƙasa da ke Abuja ta bayar da umarnin hana PENGASSAN ci gaba da yajin aikin.
Sai dai rahoton jaridar Punch ya ruwaito PENGASSAN ta bayyana cewa ba ta da masaniya kan wannan umarnin kotu, tana mai cewa ba ta hanyar shafukan sada zumunta ake isar da umarnin kotu ba.



