Gwamnatin Nijeriya ta ce kamfanin Dangote zai mayar da ma’aikatan da matatarsa ta dakatar biyo bayan samun sabani tsakanin ta da kungiyar PENGASSAN.
Ministan kwadago, Dr Mohammed Maigari Dingyadi ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da aka fitar a ranar Laraba a Abuja, inda ya ce za a biya ma’aikatan hakkokinsu ba tare da rage musu ko kwabo ba.
Haka kuma ya kara da cewa, bangarorin biyu sun cimma matsaya yayin da kungiyar PENGASSAN ta fara shirye-shiryen janye yajin aikin da ta tsunduma.



