Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatinsa ta yi kokari wajen kawo karshen matsalolin tsaro a wasu yankunan kasar.
Yayin da yake jawabi ga ‘yan kasa a bikin cika shekaru 65 da samun ‘yancin kai, ya ce zaman lafiya ya dawo a yankunan arewa maso gabas da arewa maso yammacin Najeriya.
A cewar sa, jami’an tsaro daga hukumomi daban-daban na ci gaba da jajircewa wajen ganin bayan duk wata matsalar tsaro a kasar kuma suna samun dimbin nasarori, kamar yadda Channels TV ya wallafa.



