Tuni aka fara tantance wadanda ake ganin yiwuwar za su maye gurbin shugaban hukumar zabe ta Najeriya (INEC) gabanin Shugaba Tinubu ya tuntubi majalisar kasa.
Jaridar Punch ta ruwaito wata majiya mai karfi na tabbatar mata da cewa, ofishi Sakataren gwamnatin tarayya ya fara shirya katin gayyatar zaman tantancewa yayin da hukumar tsaro ta farin kaya DSS ke cigaba da tantance ‘yan takarar.
Majiyar ta kuma kara da cewa, cikin sunayen da aka mika domin tantancewar akwai yiwuwar samun wadanda aka sani daga cikin su.



