Kamfanonin samar da hasken wutar lantarki a Najeriya sun bukaci gwamnatin ƙasar ta kawo musu dauki cikin gaggawa domin ceto su daga halin durkushewa.
Wannan ya zo a daidai lokacin da kungiyar kamfanonin ta taya shugaba Tinubu da sauran ‘yan Najeriya murnar cika shekaru 65 da samun ‘yancin kai.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa cikin sakon da sakatariyar kungiyar Dr. Joy Ogaji ta fitar, kungiyar ta yaba wa matakan da gwamnatin Tinubu ke dauka wajen daidaita al’amuran da suka shafi lantarki, sai dai ta ce akwai sauran aiki a gaba.
Dr. Joy ta ce matsalolin tulin bashi da kuma rashin kyakkyawan tsarin gudanarwa na zama babbar barazana ga ci gaban ayyukansu.



