Hukumar kula da shige da fice ta Najeriya ta bayyana cewa daga yau 1 ga watan Oktoba za ta fara farautar wadanda wa’adin bizarsu ya kare, kuma su ke ci gaba da zama a kasar, ba tare da yin abin da ya dace ba.
Kafin wannan lokaci dai gwamnatin Najeriya ta bayar da kariya na tsawon watanni uku ga wadanda wa’adin bizar ta su ya kare.
Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Akinsola Akinlabi ta fitar, ta bayyana cewa farautar za ta mayar da hankali wajen zakulo ‘yan Ć™asashen waje da suka karya dokar zama a Najeriya, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Kazalika ta ce hukuncin da za a dauka kan wadanda aka kama, ya hadar da biyan tara, mayar da su ainahin kasashensu har ma da haramta shigowa Najeriya.



