DCL Hausa Radio
Kaitsaye

‘Yansanda za su fara kamen masu amfani da bakin gilashin mota ba tare da izini ba a Najeriya

-

Babban sufeton ‘yan sandan Najeriya Kayode Egbetokun ya bayyana cewa daga ranar Alhamis 2 ga watan Oktoba, jami’ansu za su fara kamen masu amfani da bakin gilashin mota ba tare da izini ba a fadin kasar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ta kasa ASP Mohammed Halima ta fitar, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Google search engine

Sanarwar ta bayyana cewa matakin na kan tsarin dokar haramta amfani da bakin gilashin mota ta shekarar 2004, a yunkurin tabbatar da zaman lafiya da magance ayyukan laifi.

Haka kuma,  ta ce wa’adin da aka bai wa masu motoci domin sabunta takardun izini ya kare, saboda haka wajibi ne kowa ya bi doka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Za mu fara hukunta duk wani dan kasar waje da wa’adin bizarsa ya kare a Nijeriya kuma ya ci gaba da zama – Gwamnatin...

Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa yanzu tana da cikakken tsarin gano tare da cafke baƙin ƙasashen waje da suka wuce wa’adin zaman da aka ba...

Obasanjo ya nuna jarumtaka da sadaukarwa wajen yi wa Nijeriya hidima – Shugaba Tinubu

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, ya taya tsohon shugaban ƙasar Olusegun Obasanjo murnar cika shekaru 89 da haihuwa. A cikin wata sanarwa da mai magana da...

Mafi Shahara