Kwamitin majalisar wakilan Najeriya mai kula da harkokin ƙasashen ketare ya bayyana shirin fara gudanar da bincike kan zargin almundahanar wasu kudade da aka yi tsakanin shekarar 2021 zuwa 2024.
Ana zargin batan Dala 172,000 ne da aka ware wa ofisoshin jakadancin Najeriya da ke Vietnam, China da kuma Koriya ta Kudu.
Yayin da yake zantawa da jaridar Punch, shugaban kwamitin Oluwole Oke ya ce tuni aka gayyaci dukkanin masu ruwa da tsaki a lamarin don gano yadda wadannan kudade suka bace.



