Iyalan Maryam Sanda, wadda aka yanke wa hukuncin kisa a shekarar 2020 bisa laifin ajalin mijinta, ne suka sake neman gwamnati ta yi mata afuwa bisa hujjar cewa hakan zai kasance maslaha ga ’ya’yanta biyu.
Maryam, mai shekaru 37, ta shafe shekaru shida da watanni takwas a Suleja Medium Security Custodial Centre tun bayan yanke mata hukunci.
Iyalan nata sun bayyana cewa Maryam ta nuna nadama sosai, ta kuma canza salon rayuwarta, inda ta zama misali ga sauran fursunoni saboda kyakkyawan hali da biyayya ga doka a lokacin zaman gidan yari.
A bayanai na baya-bayan nan, da fadar shugaban kasa ta fitar ta hannun Hadimin shugaba Tinubu kan harkokin yada labarai Bayo Onanuga an lura da sunan Maryam a jerin wadanda aka sassautawa hukuncin zuwa daurin rai da rai daga hukuncin kisa na baya.



