Tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya bayyana shugaban Nijeriya Bola Tinubu a matsayin babbar kyauta da Allah ya ba Nijeriya domin gyaran kasar.
Yahaya Bello ya faɗi haka ne a yayin wani gangamin nuna goyon baya ga shugaba Tinubu da gwamnan Kogi Usman Ododo da aka gudanar a ranar Asabar, wanda aka watsa kai tsaye a gidan talabijin na TVC.
A cewarsa, gyaran ƙasa yana ɗaukar lokaci saboda matsalolin da aka gada, yana kuma roƙon ‘yan Nijeriya su ba shugaba Tinubu goyon baya domin cika alkawurran da ya dauka
Tsohon gwamnan ya jaddada cewa Tinubu kyauta ne daga Allah ga yan Nijeriya domin gyaranta, ya kuma yaba wa gwamnatin Tinubu bisa sauye-sauyen da ta aiwatar, ciki har da cire tallafin mai, samar da rancen kudi na karatu ga ɗalibai, da sauran su.