DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Dangote ya mayar da martani ga kamfanin NNPCL kan bashin dala biliyan 1

-

Aliko Dangote 

Matatar mai ta Dangote ta yi karin haske kan hadin gwiwarta da kamfanin mai na Nijeriya NNPCL, inda ta bayyana cewa ta amince da sayar da hannun jarin kashi 20 cikin 100 kan kudi dala biliyan 2 da miliyan 76.

Matatar ta Dangote ta yi karin haske ne, bayan wata sanarwa da aka fitar cewa kamfanin NNPCPL ya samu rancen dala biliyan daya domin tallafawa aikin matatar ko da za ta fuskanci wasu matsalolin kudi.

Google search engine

A wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba babban jami’in yada labarai a matatar, Anthony Chiejina, ya bayyana maganar a matsayin yaudara, yana mai cewa daga cikin dala biliyan 2 da miliyan 76, an amince da cewa NNPCL zai biya dala biliyan 1 ne kawai yayin da zai biya sauran a tsawon shekaru 5 ta hanyar cire danyen man da suke samarwa matatar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Har yanzu bamu kammala bincike ba shiyasa bamu gurfanar da El-rufa’i a gaban kotu ba – EFCC

Hukumar EFCC, mai yaki a cin hanci da rashawa a Nijeriya ta bayyana dalilin da ya sa har yanzu ba ta kai tsohon gwamnan Kaduna,...

Wanene sabon Shugaban Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya, Olatunji Disu?

AIG Olatunji Disu ya kasance gogaggen jami’i wanda aka nada don jagorantar rundunar 'yan sandan kasar a matsayin IGP na 23. A cewar fadar shugaban...

Mafi Shahara