DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Kungiyar ASUU ta janye yajin aikin gargadin da ta tsunduma

-

Kungiyar malaman jami’o’i ta Nijeriya ASUU ta janye yajin aikin gargadin da ta tsunduma.

Shugaban kungiyar Farfesa Chris Piwuna ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai da ya gudana a ranar Laraba, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Google search engine

Labari mai alaka: ASUU ba ta da hujjar shiga yajin aiki domin mun biya dukkanin bukatunta – Gwamnatin Nijeriya

A cewar sa, daukar matakin ya biyo bayan wani zama da kwamitin zartarwar kungiyar ya gudanar, bayan samun martani daga bangaren gwamnati kan bukatunsu.

Haka kuma, ASUU ta ce iyaye, dalibai da kuma kungiyar kwadago ta NLC sun taka rawar gani wajen sake bibiyar yajin aikin gargadin da ta yi niyyar gudanarwa na tsawon makonni biyu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Har yanzu bamu kammala bincike ba shiyasa bamu gurfanar da El-rufa’i a gaban kotu ba – EFCC

Hukumar EFCC, mai yaki a cin hanci da rashawa a Nijeriya ta bayyana dalilin da ya sa har yanzu ba ta kai tsohon gwamnan Kaduna,...

Wanene sabon Shugaban Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya, Olatunji Disu?

AIG Olatunji Disu ya kasance gogaggen jami’i wanda aka nada don jagorantar rundunar 'yan sandan kasar a matsayin IGP na 23. A cewar fadar shugaban...

Mafi Shahara