Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya rantsar da Farfesa Joash Amupitan, SAN, a matsayin sabon shugaban Hukumar Zaɓen Nijeriya, INEC.
An gudanar da rantsuwar ne da misalin ƙarfe 1 da minti 50 na rana a dakin taro na fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, inda Farfesa Amupitan ya ɗauki rantsuwar aiki a gaban shugaban ƙasa.
Tinubu ya bukace shi da ya kare mutuncin zaɓen Nijeriya da tsarin gudanar da shi, tare da ƙarfafa ingantaccen tsarin gudanarwa a hukumar INEC domin tabbatar da gaskiya da adalci a zaɓe mai zuwa.



