![]() |
Hukumar FCTA |
Hukumar lura da babban birnin tarayya Abuja ta bayyana shirinta na aiwatar da dokar hana tallace-tallace a harabar ofisoshin gwamnati.
Shugaban sashen tsaro na cikin gida, na hukumar tsaron farin kaya Sunday Olubiyi, ne ya bayyana haka yayin ganawa da manema labarai ranae Talata a Abuja.
A ranar Lahadi ne, hukumar ta FCTA ta yanke shawarar kara tsaurara matakan tsaro a harabar ofisoshin gwamnati da kewaye, domin dakile sace-sace da sauran laifuka.