DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Hukumar NEMA ta karbi ‘yan Nijeriya 150 da suka makale a Nijar

-

Hukumar ba da agajin gaggawa ta Nijeriya NEMA ta bayyana karbar ‘yan kasar 150 da suka makale a kasar Nijar.

Bayanin na kunshe ne cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a shafinta na X, inda ta ce ‘yan Nijeriyar sun sauka a filin jirgin sama na Aminu Kano, da ke jihar Kano.

Google search engine

Labari mai alaka: Hukumar NEMA ta karbi ‘yan Nijeriya 147 da suka makale a Libya

Jaridar Punch ta ruwaito cewa wannan mataki yana cikin shirin mayar da mutane ainahin kasashensu, hadin gwiwa da gwamnati tare da majalisar dinkin duniya.

Hukumar NEMA ta ce cikin wadanda aka dawo da su akwai maza 88 da mata 32, sai kuma yara maza 14 da yara mata 16.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Shugaba Bola Ahmad Tinubu ya yi ganawar sirri da sabbin hafsoshin tsaro a Abuja

Taron, wanda ya gudana kwanaki uku bayan sanar da sabbin nade-naden, shi ne karo na farko da shugaban kasa ya gana da manyan hafsoshin rundunonin...

Paul Biya ya yi wa masu zanga-zangar sakamakon zabe shagube a Kamaru

Shugaban ƙasar Kamaru, Paul Biya, ya yi shagube ga rikicin siyasar da ke faruwa bayan ayyana shi a matsayin wanda ya lashe sakamakon zaɓen shugaban...

Mafi Shahara