Jigo a jam’iyyar PDP a Nijerita Alhaji Sule Lamido ya bayyana kudirinsa na sayen tikitin neman zama sabon Shugaban jam’iyyar PDP na kasa
A wani takaitaccen rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook ya ce kudurinsa na ganin an dawo da martabar dimokuraɗiyya da kuma farfaɗo da jam’iyyar zuwa darajar da take da ita a da, ba zai taɓa yankewa ba.
Tsohon gwamnan na Jigawa na cikin sahun farko na wadanda aka kafa jam’iyyar ta PDP da su a Nijeriya.
Kuma na gaba-gaba a takarar neman zama sabon shugaban jam’iyyar ta PDP daga Arewa maso Yamma.



