Dagewar ta zo ne ’yan sa’o’i bayan tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya ayyana shirinsa na takarar shugabancin jam’iyyar, duk da cewa wasu ’yan yankin Arewa maso Yamma na jam’iyyar sun riga sun amince da tsohon minista Kabiru Tanimu Turaki (SAN) a matsayin ɗan takarar da aka amince da shi.
Kodayake, wasu bangarori na PDP, ciki har da masu goyon bayan Lamido da Nyesom Wike, sun ƙi amincewa da wannan yarjejeniya, lamarin da ke nuna rikici da rarrabuwar kai a cikin jam’iyyar a daidai lokacin da muhimman mambobi ke ficewa.
Shugaban Kwamitin Shirya Taron Gangamin Kasa kuma Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ne ya sanar da hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Litinin, inda ya ce wasu dalilai ne na ba-zata suka sa aka jinkirta taron.
Fintiri ya bayyana cewa za’a sanar da sabuwar ranar taron a nan gaba, ya kuma tabbatar da cewa kwamitinsu na da cikakken kudiri na gudanar da taron gangami cikin gaskiya da lumana.
Rahoton jaridar Punch ya ce ana sa ran PDP za ta gudanar da taron gangamin zabenta tsakanin 15 zuwa 16 ga Nuwamba, 2025 a Ibadan, Jihar Oyo.



