DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Shugaba Bola Ahmad Tinubu ya yi ganawar sirri da sabbin hafsoshin tsaro a Abuja

-

Taron, wanda ya gudana kwanaki uku bayan sanar da sabbin nade-naden, shi ne karo na farko da shugaban kasa ya gana da manyan hafsoshin rundunonin tsaron ƙasar tun bayan sauye-sauyen da aka yi.

A cewar fadar shugaban kasa, wannan sabon tsarin nadin hafsoshin tsaro na daga cikin matakan da gwamnati ke ɗauka don ƙarfafa ƙwarewa, ƙara wa sojoji kwarin gwiwa da kuma inganta haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro.

Google search engine

Cikin waɗanda suka halarci taron akwai Babban Hafsan Tsaro, Janar Olufemi Oluyede; Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Mejo Janar Waheedi Shaibu; Babban Hafsan Sojin Sama, Air Vice Marshal Kennedy Aneke; da kuma Babban Hafsan Rundunar Ruwa, Rear Admiral Idi Abbas.

Jaridar The Nation ta ce Babban Daraktan Leken Asiri na Sojoji, Mejo Janar Emmanuel Undiendeye, wanda ya ci gaba da rike mukaminsa, shima ya halarta.

Ko da yake ba a bayyana cikakken jawabin shugaban kasa ga sabbin hafsoshin ba, majiyoyi daga Villa sun ce tattaunawar ta fi karkata kan muhimman batutuwan tsaro, yaƙi da ta’addanci, da kuma yadda gwamnati ke ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a fadin ƙasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Paul Biya ya yi wa masu zanga-zangar sakamakon zabe shagube a Kamaru

Shugaban ƙasar Kamaru, Paul Biya, ya yi shagube ga rikicin siyasar da ke faruwa bayan ayyana shi a matsayin wanda ya lashe sakamakon zaɓen shugaban...

Kungiyar kwallon kafa ta Juventus ta sallami mai horaswarta Igor Tudor

Kungiyar Juventus ta sallami kocinta Igor Tudor a ranar Litinin bayan shan kashi da ci 1-0 a hannun Lazio, wanda ya sa kungiyar ta tara...

Mafi Shahara